An Gargaɗi Mambobin Kungiyar Dillalan Fetur Da Iskar Gas Na Arewa Kan Cika Ka’idojin CAC

Kungiyar Dillalan Man Fetur Da Iskar Gas Ta Arewa ta bukaci daukacin mambobinta da su gaggauta mika bayanansu na shekara ga hukumar CAC.

Alfijir Labarai ta rawaito shugaban kungiyar Alh, Bashir Ahmad Danmalam, ya jaddada muhimmancin bin ka’idojin da dokokin hukumar CAC, domin tabbatar da kare kasuwancinsu.

Ya Kara da cewar kin biyayya ga
Ga tsarin miki bayanan hadan hadarsu na shekara-shekara, kamar yadda CAC ta umarta, na nuni da tsayawar wannan kasuwancin.

Sakamakon haka, hukumar CAC na iya canza matsayin kamfani ko kasuwanci zuwa wanda ya daina aiki, ciki har da Yiwuwar goge rajistarsa.

Danmalam ya bukaci kamfanonin da suka yi rajista, tun daga kanana zuwa manyan kamfanoni, da su yi biyayya ga umarnin CAC.

Ya sake jaddada cewa wajibi ne a gabatar da miki bayanan kamfani na shekara-shekara ba tare da la’akari da ko kasuwancin yana aiki sosai ba.

Kamar yadda ke kunshe cikin dokokin hukumar ta CAC, za a buƙaci ko wane kamfani da su biya wasu kudade a bisa girman kamfani.

Saboda haka, dole ne ko wanne kamfani ya guje miki bayanansu a makare, domin kaucewa cin tarar Naira 5000.

Yana da mahimmanci a fayyace cewa bayana kamfani na shekara-shekara ba haraji ba ne.

Miki waɗannan bayanai a kan lokaci yana nuna cewa kamfanoni na aiki a ko da yaushe, wanda zai basu damar ci gaba da kasancewar a rumbun adana bayanai na CAC.

Kungiyar dillalan mai da iskar gas ta Arewa CAC, ta dauki wannan al’amari da muhimmanci, domin ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancinsu karkashin dokoki da tsare tsare-tsaren hukumar.

Kiran na Danmalam ya zo ne a matsayin tunatarwa a kan lokaci ga dukkan mambobin kungiyar, domin su gaggauta sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, tare da tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukansu da bin doka da oda a kasuwanci.

Wa’adin mika bayanan shekara ya kure, domin haka ake shawartar mambobin kungiyar da su yi kokarin cika ka’idojin hukumar ta CAC tare da kare harkokin kasuwancinsu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI

One Reply to “An Gargaɗi Mambobin Kungiyar Dillalan Fetur Da Iskar Gas Na Arewa Kan Cika Ka’idojin CAC”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *