An kwantar da tsohon shugaban Najeriya Buhari a ICU a Landan – Rahoto

FB IMG 1751448763305

Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na fama da rashin lafiya, kuma rahotanni sun ce kwanan nan aka sallame shi daga dakin kula da masu matsananciyar rashin lafiya  (ICU) a wani asibiti da ke Landan a kasar Birtaniya.

Jaridar TheCable ta rawaito daga Empowered Newswire, wani makusancin tsohon shugaban ya bayyana cewa Buhari ya kamu da rashin lafiya ne a Landan yayin da ya je don duba lafiyarsa.

Rahoton ya ce an kwantar da Buhari a dakin ICU, amma daga bisani aka sallame shi makon da ya gabata.

Ko da ya ke ba a bayyana irin cutar da ke damunsa ba, rahotanni sun nuna cewa yana samun sauki a Landan, kuma ana sa ran zai dawo Najeriya da zarar ya warke gaba ɗaya.

Empowered Newswire ta kara da cewa, bisa bayanan da suka samu daga wasu majiyoyi masu tushe, Mamman Daura – kawun Buhari kuma amintaccensa – shima yana samun sauki daga rashin lafiya a kasar Birtaniya.

Buhari bai halarci bikin cika shekaru 50 da kafuwar Kungiyar raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS) da aka gudanar a Legas ranar 28 ga Mayu ba.

A wata wasika da ya aika wa Shugaba Bola Tinubu, Buhari ya bayyana cewa rashin halartar sa taron ya samo asali ne daga tafiyarsa ta duba lafiya a Birtaniya.

Daily Nigerian

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *