An Rantsar Da Bola Tinubu A Matsayin Shugaban Nijeriya


Alfijr ta rawaito Tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ne ya mika masa mulkin ga sabon shugaban kasa.

An rantsar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban Nijeriya.

Alkalin Alkalan Nijeriya ne ya rantsar da shi a dandalin Eagle da ke Abuja.

Sa’annan shi ma Kashim Shettima an rantsar da shi a matsayin mataimakin shugaban kasa.

A halin yanzu Tinubu shi ne shugaban Nijeriya na 16 kuma ya maye gurbin tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *