Ana Wata! An tsige mataimakin shugaban makaranta saboda taɓa wa ɗaliba ƙirji

FB IMG 1759238267904

Hukumar Ilimi ta Ghana (GES) ta kori Charles Akwasi Aidoo, mataimakin shugaban makarantar sakadire ta Kwame Nkrumah da ke a Jami’ar Kimiyya da fasaha ta Kwame Nkrumah bayan wani bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta da ke nuna yana taɓa wa wata ɗaliba mace ƙirjinta a wani wuri da ake ganin ofishinsa ne.

A cikin wani bidiyon mai tsawon dakika 16 da ɗalibar ta ɗauka, an ga Aidoo yana sanya kansa a kafadar ɗalibar.

A cikin wata sanarwa, hukumar ta ce: “Gwamnati, a cikin ƙudurinta na kare martabar aikin koyarwa da jin daɗi da kare lafiyar ɗalibai, ta cire mataimakin shugaban makarantar daga muƙaminsa.”

Haka kuma, hukumar ta ƙara da cewa: “Mun haramta wa Charles Akwasi Aidoo shiga makarantar yayin da bincike ke gudana bisa ka’idojin hukumar.”

Sanarwar ta bayyana cewa hukumar za ta bi dukkan matakai na doka don tabbatar da cewa an hukunta shi bisa ga ka’idojinta.

Hukumar ta ƙara da cewa suna ƙin duk wani aiki da zai kawo barazana ga lafiya da mutunci da kuma jin daɗin ɗalibai.

Ba wannan ne karo na farko da hukumar ke ɗaukar mataki kan malamai ko shugabannin makarantu da suka aikata “aikin rashin ɗa’a” da ɗalibansu ba.

A watan Nuwamba 2018, hukumar ta kori malamai tara da wasu manyan ma’aikata a wasu makarantu sakamakon aikata batsa da rashin ɗa’a.

BBC

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *