Ana Wata! Kotu Ta Dakatar Da Gwamnatin Kano Rushe Masarautun Jihar

IMG 20240524 WA0022

Daga Aminu Bala Madobi

Tun bayan bayyanar sabbin masarautu da tsohuwar gwamnatin tsohon gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje tayi ake cigaba da kai ruwa rana game da halaccin samuwar masarautun masu daraja ta daya(1)

Sai dai bayan tafiya-tai-tafiya, Sabuwar gwamnatin Abba Kabir Yusuf ke nuna shakku kan halaccin kirkiro wadannan masarautu, tare da rashin sanin dalilin tunbuke sarki sanusi na biyu awancan lokaci.

Tunbuke sarki sanusi da tsohuwar gwamnatin baya tayi a cewar gwamnatin Abba Kabir yace anyi lamarin ne cikin garaje.

Alfijir labarai ta rawaito Aminu Babba Dan agundi ya garzaya kotu domin bin kadin shirin rushe masarautu da gwamnatin Kano ta kudiri aniyar aiwatar wa.

A zaman shari’ar na ranar Alhamis 23 ga watan Mayun 2024 karkashin Mai sharia A. M. Liman, kotun ta zayyana umarnin wucin gadi guda 8 ga wadanda suke takaddama (Dan agundi & Kano).

A zaman kotun na yau, kotun ta bada umarnin kowa ya tsaya a matsayin sa, har izuwa lokacin da za a sake sauraron shariar a ranar 3 ga watan Yuni 2024.

Shi dai Aminu Babba na karar gwamnatin jihar Kano, Majalisar dokokin Kano, da kakakin majalisar dokoki da kwamishinan ‘yansan Kano da babban sifeton ‘yansanda har da ma Shugaban hukumar tsaron farin kaya DSS.

Kotun ta bada umarnin wucin-gadi ga mai kara (Dan agundi) da  wadanda ake kara na 5 da na 8, na kada su wajabta ko tursasa halaccin bin dokar masarautu da akayi a 2019.

Kotun ta kuma umarci wadanda ake kara na 5,
6,7 da na 8 dasu tabbatar an samar da ingantaccen tsaro gabanin yanke hukunci kan wannan kara.

IMG 20240523 WA0157
Order
IMG 20240523 WA0159
Order
IMG 20240523 WA0160
Order
IMG 20240523 WA0158
Order

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/F9mRRuOf58G3MlLKsNCJbL

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *