Ana Wata! Yan Yahoo Sun Kutsa Wayoyin Aliko Dangote Da Femi Otedola

IMG 20251119 WA0138

Daga Aminu Bala Madobi

— Manyan Attajiran Najeriya Sun Fuskanci Barazana

A wani lamari da ya girgiza harkar tsaro ta intanet a Najeriya, wasu gungun masu kutse (hackers), da ake zargin yan Yahoo ne, sun yi nasarar shiga wayoyin manyan attajiran kasar nan — Aliko Dangote da Femi Otedola.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kutsa wayar Dangote sau biyu a cikin kwanaki biyu, yayinda aka kutsa ta Otedola sau ɗaya.

Binciken DRC Hausa ya bayyana cewa masu kutsen sun yi amfani da dabaru na zamani wajen shiga tsarin wayoyin, inda suka samu damar ganin bayanai da saƙonnin sirri.

Bayan haka, masu kutsen suka nemi kuɗin fansa (ransom) domin su Dakatar da yin kutsen cikin wayoyin manyan attajiran idan kuma abin ya gagara su cigaba da satar bayanan da suka samu ko kuma su kwace cikakken ikon wayoyin.

Har izuwa yanzu ba a bayyana ko wanne irin bayanai ne aka sace ba, ko na kasuwanci ne, ko na sirri. Haka kuma ba a tabbatar da ko Dangote da Otedola sun sake samun cikakken iko da wayoyinsu ba.

Masana harkar tsaro suna kallon wannan lamari a matsayin kira ga gwamnati da manyan ‘yan kasuwa su dauki tsaro na intanet da matuƙar muhimmanci. A cewarsu, ya kamata mutane, musamman shugabanni da attajirai, su kara taka-tsantsan wajen amfani da bayanansu a wayoyi masu haɗuwa da intanet.

Lamarin ya kuma jawo zazzafar tattaunawa a dandalin sada zumunta, inda mutane da dama ke bayyana damuwa kan yadda hare-haren cyber ke karuwa a Najeriya. Wasu kuma na bayyana mamakinsu cewa maharan suka iya kutsa cikin wayoyin attajirai da ke da tsauraran tsare-tsare.

Duk da cewa har izuwa yanzu hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken sanarwa ba, ana sa ran hukumar EFCC da sauran jami’an tsaro za su fara gudanar da bincike kan lamarin nan ba da jimawa ba.

— Zamu ci gaba da kawo muku cikakkun bayanai yayin da labarin ke cigaba da tasowa.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *