APC na amfani da bangaren shari’a domin shafe jam’iyyun hamayya – Atiku Abubakar

Atiku Abubakar

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben da ya wuce , Atiku Abubakar ya yi zargin cewa jamiyyar APC mai mulki na amfani da bangaren sharia da nufin murkushe jam’iyyun hamayya.

Alfijir Labarai ta rawaito tsohon mataimakin shugaban kasa ya yi misali da hukuncin da kotunan daukaka kara suka a yanke a wasu jihohi, ciki har da Zamfara da Filato da Kano da Nasarawa, yana cewa gwamnati na rabewa ne da shari`a wajen kwace jihohin da ke karkashin ikon jam’iyyun adawa.

Sai dai jam’iyyar APC ta musanta zargin

Atiku Abubakar ya ce sun lura da take-taken jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, kuma sun fahinci cewa da sannu tana nema ta murkushe hamayya baki daya.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi zargin cewa APC na amfani da karfi wajen yin magudi ko rabewa da bangaren shari’a wajen soke nasarar da `yan hamayya suka samu a wasu jihohi, ciki har da jihohin Kano da Zamfara da Filato da kuma Nasarawa.

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

Mataimaki na musaman ga Atiku Abdurrashid Shehu ya shaida wa Alfijir Labarai cewa Jam’iyyar APC mai mulki na kokarin karya dimokradiyya kasar ne

” Wannan bangare na sharia, bangare ne da yake cin gashi kansa amma yadda mu ke zargin sun yi kutse wajan shiga wannan bangare tare da yin kokari da yukurin karbar wasu jihohi, idan ka duba jihohi ne da suka fito daga jam’iyyun hammaya”, in ji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *