APC Ta Buƙaci INEC Ta Bayyana Zaɓen Kano A Matsayin Inconclusive ko Ta Tafi Kotu


Alfijr ta rawaito jama’iyar APC mai mulki a jihar Kano, ta ja hankalin hukumar INEC kan ta ayyana sakamakon zaɓen gwamnan jihar a matsayin wanda da bai kammala ba ko kuma jam’iyyar ta garzaya kotu.

Lauyan jama’iyar Barisata Abdul Fagge, ne ya yi jan hankalin yayin wani taron manema labarai da jam’iyyar ta gudanar da yammacin yau Talata.

Ya ce, yayin zaɓen an samu ɓarkewar rikici a wasu yankunan wanda hakan ya sanya aka soke kuri’un da aka kaɗa sai dai yayin sanar da sakamakon ba a yi la’akari da hakan ba.

Haka kuma lauyan, ya ƙara da cewa jama’iya APC za ta bi dukkan matakan da doka ta tanada domin ganin an sake zaben a wurarren da aka samu waɗannan matsaloli.

Da yake jawabi yayin taron ɗan takarar gwamna a zaɓen, mataimakin gwamnan Kano Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna, ya fara da yaba wa mutanen jihar Kano musamman ma waɗanda suka kaɗa masa ƙuri’arsa.

Gawuna ya ƙara da cewa, jam’iyyar tasu ta yi nazari sosai kan abubuwan da suka faru a kan zaben tare da shiin daukar matakin doka don bin kadun al’ummar jihar Kano da suka kada musu kuri’a.

KAKAKI Hausa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ


2 Replies to “APC Ta Buƙaci INEC Ta Bayyana Zaɓen Kano A Matsayin Inconclusive ko Ta Tafi Kotu

  1. Kafin aje kotun. Kamata yayi duk wadanda aka kama da kokarin fasa akwatunan zabe a baiyanasu. Da Kuma sunayen wadanda suka turasu Kuma Yan wache jamaiya che

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *