Sakon Zababben Gwamnan Kano
Engr. Abba k. Yusuf Ga Al’ummar Kano Da Kasa

Alfijr ta rawaito zababben gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya bukaci magoya bayan sa da ‘ya’yan jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) da su shiga addu’o’in Allah ya ba shi basira da kuma yi masa jagora wajen ganin ya samar da ribar Dimokraɗiyya ga al’ummar Kano.

Ya ƙara da cewar addu’o’in sun wadatar a matsayin nuna goyon baya da kuma murnar nasarar da ya samu a zaben ranar Asabar, kuma addu’ar ta fi tsawon tafiyar da wasu masu kishinsa ke yi a wasu sassan ƙasar nan musamman ganin halin da ake ciki na rashin tsaro tare da ‘yan fashi da garkuwa da mutane da ta’addanci a fadin kasar nan.

Da yake mika godiyarsa ga magoya bayansa a ciki da wajen jihar Kano, zababben gwamnan ya bukaci masu tattakin da su daina tafiya domin hakan ba zai taimaka ba yadda ya kamata wajen magance dimbin kalubalen tattalin arziki da zamantakewa da ke jiran gwamnati mai jiran gado bayan ya karbi ragamar mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Sanarwa mai dauke da sa hannun Sanusi Bature Dawakin Tofa, Kakakin zababben gwamnan jihar H.E. Engr. Abba K. Yusuf ya ce, gwamnatin jihar Kano mai jiran gado za ta himmatu wajen samar wa al’umma gaba ta fuskar tsaro, lafiya, ilimi, tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa da kyautata jin dadin tsofaffi, ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu a matsayin taken Engr. Abba ya jagoranci gwamnati.

A matsayinsa na Gwamnan Kano mai kishin al’ummar Kano, Engr. Abba ya ɗora hannu da hannu wajen tabbatar da ganin an tabbatar da tafiyar Kwankwasiyya da kuma manufofin NNPP na samar da ingantaccen jagoranci mai aiki ga kowa da kowa a jihar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *