AROGMA Ta Bukaci Majalisar Dattijai Ta Bincika Yadda NIPCO Ta Murkushe Hannun Jarin Dillalan Man Fetur

IMG 20231211 WA0016

Shugaban kungiyar dillalan man fetur da iskar Gas ta Arewa (AROGMA), Bashir Ahmad Danmalam, ya bukaci majalisar dattawan Najeriya da ta binciki kamfanin mai na Najeriya NIPCO bisa zargin rike hannun jarin da ‘yan kasuwar man suka zuba sama da shekaru 20.

Alfijir labarai ta rawaito cikin wata sanarwa da Alh Bashir Danmalam ya raba wa manema labarai, ya yi kira ga Majalisar Dattawa da Kamfanin NNPC da su shiga tsakani tare da yin karin haske kan batun hannun jarin da ‘yan kasuwar man suka zuba a shekaru 20 da suka gabata, yana mai jaddada cewa babu wani amfani ko daya da yan kasuwar suka samu a tsawon wannan lokacin.

A cewar Danmalam, ‘yan kasuwar man Najeriya sun shiga rudani kan halin da hannayen jarin su ke ciki a NIPCO.

Ya bukaci kamfanin NNPC da ya dakatar da ba su Kayayyakin har sai an warware matsalar hannun jarin.

Shugaban na AROGMA ya kuma yi kira ga Majalisar Dattawa da ‘Yan Majalisu da su binciki abin da NIPCO ta yi, inda ya ce duk da dimbin jarin da aka zuba, da alama hannayen jarin ba su da bambanci da takardar tsire.

Ya kuma yi nuni da irin halin rashin da’a da ake ciki inda ‘yan kasashen waje ne kawai ake ganin suna cin gajiyar hannun jarin da ‘yan kasuwar man Najeriya suka zuba tare da hadin gwiwar ‘yan Najeriya kalilan, wadanda wasu daga cikinsu sun mutu ba tare da cin gajiyar komai ba sama da shekaru ashirin.

Danmalam da yake bayyana damuwarsa ga talakawan kasar ya jaddada rawar da majalisar dattawa ke takawa wajen kare muradun ‘yan Najeriya a matsayin masu yin doka. Yayi kira da a binciki tsirarun mutanen da kila sun hada kai da Yan kasashen wajen domin damfarar talakawa da daruruwan yan kasuwar mai.

Shugaban na AROGMA ya nemi hukumat NNPC da ta daina ba da Kayayyaki ga NIPCO har sai an mayar da hannun jarin da aka ajiye ga masu zuba jari.

Danmalam ya jaddada cewa har yanzu ba a san halin da hannayen jarin suke ciki ba, domin har yanzu ba su shiga kasuwa ba.

AROGMA ta himmatu wajen daukar matakan da suka dace domin tabbatar da an yi adalci, tana mai cewa NIPCO ta hada kai da daidaikun mutane, da suka hada da Yan kasa masu San kansu da kuma baki, ba tare da biyan bukatun da aka yi alkawari ba ga wadanda suka saka hannun jarin su.

Danmalam ya ce idan matsalar Rashin lafiya ta sameka ko mahaifinka kaje kayi kokarin sayar da hannun jari don magance matsalar kudin magani, hannun jarin da muke da shi a NIPCO ba zai amfanar da komai ba.

Ya kalubalanci NIPCO da ta kai hannun jarin kasuwa kuma ya tabbatar da cewa ba za a iya siyar da su ba.

A karshe ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta daina duk wata alaka da kamfanin NIPCO ko jami’anta domin kare hakkin jama’a.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *