Kungiyar dillalan man fetur da iskar gas ta Arewa (AROGMA) ta nesanta kanta daga shirin tsundima yajin aikin da kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya NUPENG ta shirya yi a ranar 8 ga watan Satumba.
Cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar AROGMA, Bashir Ahmad Danmalam ya sanyawa hannu kuma aka raba wa manema labarai.
Danmalam ya yi kira ga direbobin tankokin dakon.man fetur na Najeriya da su yi watsi da wannan umarni na NUPENG.
Ya ce “mafi yawan ‘ya’yan kungiyar NUPENG suna kan albashin gwamnati’.
A cewar Danmalam, “Ta yaya akasarin ‘yan Najeriya da ba za su iya samun abin dogaro da kai ba sai sun fita anyo fafutuka kullum, ciki har da direbobi da ma’aikatan mai su shiga yajin aikin da zai jefa kasar cikin mawuyacin hali?
Shugaban AROGMAn ya ci gaba da cewa ‘yan Najeriya na cikin mawuyacin hali na tattalin arziki. “Idan suka tafi yajin aiki, me ‘yan Najeriya za su samu? Wacce riba zasu samu, in ba faɗuwa ba” ‘Yan Najeriya ba su shirya yajin aikin ba.
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su marawa Dangote baya domin su ci gaba da cin gajiyar tallafin man fetur.
“Idan ‘yan Najeriya ba su marawa Dangote baya ba, kuma idan ya daina sayar da man fetur ga ‘yan Najeriya, kowa yasani lamarin ne zai tabarbare, komi zai yi tsada sosai,” in ji shi.
Ya kara da cewa Arewa Oil and Gas ba sa wani rikici da Dangote inda ya yaba masa kan yadda yake tafiyar da rarraba albarkatun man fetur.
“Idan kuna rikici da Dangote, ku je ku ci gaba da rikicin ku, amma kar ku shigo da Kungiyar mu cikin wannan lamarin.”
Bashir Danmalam ya kuma zargi kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (NUPENG) da rikon sakainar kashi kan sauye-sauyen da ke tafe a bangaren man fetur, wanda a cewarsa zai kawo karshen mulkin da suka dade suna yi.
Dan-malam ya yi zargin cewa tankiyar da NUPENG ya samo asali ne daga yadda ake shirin dakile haramtattun kudade, da sanya haraji, da kuma tauye hakkin wasu kungiyoyi. “Ba za su sake samun ikon mallaka ko mamaye masana’antar ba,” in ji shi.
Daganan Dan MALLAM Ya caccaki wadanda ke zargin Dangote da yunkurin mamaye bangaren jigilar man tsawon shekaru.
“Sun manta abin da suka yi wa ‘yan Najeriya, yanzu saura kiris a fitar da su gaba daya daga mamayar komi dasuka yi” in ji Danmalam.
Danmalam ya fayyace cewa matatar man Dangote ba ta haramta ayyukan kungiyar ba, amma ta bayar da shawarar cewa direbobin su kafa kungiya da wani suna na daban da Direbobin Tankar Man Fetur (PTD), reshen kungiyar NUPENG.
“Gaskiya ita ce NUPENG ba za ta iya zama ba tare da PTD ba.
Ya caccaki wadanda ke zargin Dangote da yunkurin mamaye jigilar man a fadin kasa, inda ya bayyana cewa su da kansu sun mamaye harkar man fetur din Najeriya tsawon shekaru. “Sun manta abin da suka yi wa ‘yan Najeriya, yanzu an kusa fitar da su gaba daya,” in ji Danmalam.
Danmalam ya fayyace cewa matatar man Dangote ba ta haramta ayyukan kungiyar ba, amma ta bayar da shawarar cewa direbobin su kafa kungiya da wata suna daban da Direbobin Tankar Man Fetur (PTD), reshen kungiyar NUPENG. “Gaskiya ita ce NUPENG ba za ta iya zama ba tare da PTD ba.
Danmalam ya zargi kungiyar NUPENG da kokarin yin zagon kasa ga kokarin matatar man saboda son zuciya da son rai. “Sun yi amfani da tsarin ne don arzuta kansu, su bar su su yi barci su ba da damar a kai kayayyakinmu zuwa gidajen mai ba tare da tsada ba,” inji shi.
Ya yi watsi da barazanar yajin aikin da kungiyar NUPENG ke yi, yana mai cewa hakan ba zai yi wani tasiri ba. “Ko da a cikin kungiyar, ‘yan kaɗan ne kawai ke amfana. Ban da haka, akwai rarrabuwa tsakanin PTD, Wanda kuma babbar barazana ce ga NUPENG,” in ji Danmalam.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t