Attajirin nan ɗan ƙasar Afirka ta Kudu, Johann Rupert ya zarce attajirin nan ɗan Najeriya, Aliko Ɗangote a matsayin wanda ya fi kowa arziƙi a nahiyar Afirka, kamar yadda mujallar Bloomberg Billionaires Index.
Alfijir Labarai ta rawaito mista Rupert shi ne mai kamfanin Richemont wanda ɗaya ne daga cikin manyan kamfanonin da ke samar da kayan alatu da suka haɗa da shagunan Cartier and Montblack da ke sayar da turaren da agoguna da sauransu.
Yawan kuɗin attajirin sun ƙaru zuwa dala biliyan 14.3 daga dala biliyan 1.9, abin ya sa ya zama mai kuɗin duniya na 147 inda ya bai wa Ɗangote na Najeriya tazarar mutum 12.
Arziƙin Ɗangote dai ya ragu ne da dala biliyan ɗaya da miliyan ɗari bakwai ($1.7bn) a shekarar nan ta 2024, abin da ya mayar da yawan dukiyarsa zuwa dala biliyan 13.4, in ji mujallar Bloomberg.
BBC
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj