Gwamnatin Tarayya Ta ƙaddamar da cibiyoyin fasahar kere-kere da fasahar ICT a Garin Makurdi na jihar Benue da nufin samar da ayyukan yi 40,000 a duk shekara.
Alfijir Labarai ta rawaito mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima ne ya jagoranci bikin kaddamar war wanda ya bayyana cewa wannan shiri na daga cikin manyan tsare-tsare na tattalin arziki na Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Stanley Nkwocha, babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasa ne ya sanar da wannan ci gaban a ranar 27 ga Agusta, 2024.
Shettima ya bayyana cewa, “Cibiyar za ta cika ka’idojin duniya kuma tana da damar samar da ayyuka kusan 48,000 a duk shekara a cikin jihar.”
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj