Ba Za Mu Bari Kayan Nijar Ya Shigo Mana Ta Iyaka Ba – Najeriya

Ya zama wajibi su ma shugabannin hukumomin tsaron kasashen su yi aiki tare domin aiwatar da kudirorin da aka amince da su.

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewar babu wani kunshin kayan Jamhuriyar Nijar da za ta bari ya ratsa ta cikin kasarta, sakamakon jerin takunkumin karya tattalin arzikin da kungiyar ECOWAS ta amince da shi domin ladabtar da sojojin da suka yi juyin mulki.

Ya Umarci jami’ansa wajen dakile duk wani yunkuri na saba wa umarnin shugaban kasa wajen tabbatar da rufe iyakokin Najeriya da suka hada da Nijar baki daya.

Adeniyi wanda ya ziyarci wasu iyakokin da ke arewacin Najeriya ya kuma gana da shugabannin hukumomin tsaron Jamhuriyar Benin, inda ya bukaci hadin kansu domin aiwatar da matakan da shugabannin ECOWAS suka dauka.

Shugaban ya ce shugaba Bola Tinubu da takwaransa Patrice Talon na shata sabbin yarjeniyoyin da suka hada da na tattalin arziki da tsaro wajen aiki tare, yayin da ya kara da cewa ya zama wajibi su ma shugabannin hukumomin tsaron kasashen su yi aiki tare domin aiwatar da kudirorin da aka amince da su.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *