Ba’a Taba Barayin Gwamnati Ba Kamar Na Mulkin Buhari-Bishop

Bishop na darikar Katolika dake Sokoto, Matthew Kukah, ya ce Najeriya ta fuskanci matsalar cin hanci da rashawa a gwamnatin da ta gabata karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari

Alfijir Labarai ta rawaito Kukah ya bayyana haka ne a yayin da yake gabatar da wani muhimmin jawabi a wajen bikin cika shekaru 60 na Aare Afe Babalola, a Ado Ekiti ranar Litinin

Malamin ya bayyana cewa, ba a zamanin Buhari aka fara cin hanci da rashawa ba, amma gwamnatinsa ta yi kaurin suna ta fuskar banzatar da kudi

Ya ce, Mun ga yanayin cin hanci da rashawa mafi muni a Najeriya.

Femi Falana, abokina a nan, zai yi magana a kan hakan, domin ya wallafa wasu kasidu da ya shafi abubuwan da suka faru a gwamnatin Buhari.

Ba su ne suka haifar da cin hanci da rashawa ba amma ina ganin a gwamnatin da ta gabata mun ga mafi muni na cin hanci da rashawa ko ta fuskar dabi’a, kudi da sauran sharudda inji shi

Kukah ya koka da yadda Najeriya ke raba mulkin da kundin tsarin mulki ya ba ta da yan fashi da sauran yan ta’adda

Limamin ya nuna damuwarsa kan yadda a zahiri mutanen Najeriya ke yin garkuwa da mutanen da ke barazana ga wanzuwar dimokaradiyya a kasarmu.

A cewarsa, da yawa daga cikin ‘yan Najeriya sun rasa imaninsu a fannin shari’a

Ya kamata Najeriya ta farfado bayan irin halin da gwamnatin da ta gabata ta bar kasar.

Sai dai Bishop din ya ce lokaci ya yi da za a sake gina kasar, inda ya kara da cewa ‘yan Najeriya sun saka ‘mummunan baya’ a bayansu, sakamakon sakamakon zaben 2023

Vanguard/Dimokuradiyya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *