Babban Kwamandan Hisba Ya Ja Hankalin Admin Whatsapp Na Kano

Alfijr ta rawaito Babban kwamandan Hukumar Hisbah na jihar Kano Ibni Sina ya ja hankali masu amfani da Manhajar Whatsapp da su ji tsoron Allah wajen tura sakonni masu mahimmanci da wayoyin su.

Kwamandan yayi wannan kiran ne a wata ziyarar hadin guiwa da kungiyar Admin ta jihar Kano karkashin jagorancin Ibrahim Khalil suka kaiwa hukumar a ranar Alhamis wato, Kano State Admin Forum.

Ya Kara da cewar kungiyar tayi kokarin bankado barna a duk inda take su hana iya abinda za su iya, abin da ya gagaresu kuma su sanar da hukumar domin daukar matakin daya da ce.

Ibni Sina ya ja hankalin yan kungiyar da suka kai masa ziyarar da su ji tsoron Allah wajen mu amulolinsu, sannan kuma su tuna duk sakon da suka aika a kafafen sada zumunta idan alheri ne kana da dimbin lada, haka idan Sharri ka aika haka zunubanka zu su yi ta karuwa, Sakamakon wannan abin.

A nasa bangaren shugaban kungiyar ta Admin Ibrahim Khalil ya bayyana ziyarar a wani bangare na kokarin tsaftace harkar Whatsapp a Kano, duba da yadda wasu bata gari ke kokarin cutar al umma da lalata Tarbiyya.

Ya Kara da cewar lokaci yayi da al umma zasu sauya tunaninsu wajen amfani da Whatsapp musamman a Group da ake tara al umma, ta amfani da shi wajen kasuwanci da ilimintarwa maimakon Damfara da masha’a da wasu bara gurbi ke yi.

A karshe yayi kira da dukkan wasu masu Whatsapp Group da su garzayo don shiga wannan kungiyar duba da gwamnati ce ta yi umarnin haka domin tsaftace harkar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *