Babbar Magana! Wata Hajiya Daga Najeriya Ta Kashe Kanta A Madina

Screenshot 20240610 100938 Facebook

Wasu maniyyata guda biyu ƴan asalin jihar Kwara da ke aiwatar da aikin Hajjin bana a ƙasar Saudiyya daga jihar Kwara; Salihu Mohammed da Hawau Mohammed, sun rasu a birnin Madina.

Alfijir labarai ta ruwaito sakataren zartarwa na hukumar Alhazai ta Jihar Kwara, AbdulSalam AbdulKabir, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

A cewar sa, yayin da Salihu Mohammed ya rasu a sashin kula da marasa lafiya na musamman na asibitin gwamnati da ke Madina bayan ya fara jinya cikin ƙanƙanin lokaci.

Ita kuma hukumomin ƙasar Saudiyya sun gudanar da bincike suka gano cewa Hauwa’u Mohammed ta kashe kanta ne, ta hanyar faɗowa, da gangan, daga saman benen masaukinta da ke Madina.

Hukumomin Saudiyya da na jihar Kwara sun bayyana faruwar lamarin a matsayin abin takaici gami da bakin ciki tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *