Alfijr ta rawaito ɗan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a Jam’iyyar APC, Abdulsalam Abdulkarim Zaura. Wanda aka fi sani da A.A Zaura ya sha alwashin ci gaba da kokarin ganin ya cimma burinsa na siyasa.
Baya ga haka, Zaura ya bayyana cewa ya jajirce wajen ganin ya samu nasarar gudanar da aikin da zai ba shi damar yin hidimar mazabarsa ba tare da la’akari da matsalolin siyasa ba.
Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Laraba a hedkwatar yakin neman zaben sa na titin Zaria, Kano, Zaura ya ce an kammala ayyukan rangadin yakin neman zabe a fadin unguwanni 172 da kananan hukumomi 15 da suka hada da mazabar Sanata.
Jigon na APC ya ce yana da kwarin guiwar samun nasara a zabukan da za a gudanar ta yadda ya gudanar da ayyuka da dama wadanda suka yi tasiri ga rayuwar al’ummar mazabar sa.
Ya kuma yi alfahari da cewa gangamin mutane miliyan daya da aka shirya wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed ya rufe bakin jam’iyyun adawa a jihar.
A cewarsa, “Nan da ‘yan kwanaki za mu fito da shirin mu na fara yakin neman zabe a fadin kananan hukumomi 16 da kuma unguwanni 172 da suka hada da mazabar Kano ta tsakiya.
Mun shirya tsaf kuma a shekarar 2023 muna da kwarin gwiwar samun nasara saboda mun taba rayuwar al’ummarmu kuma mun san matsalar mutanenmu.
“Ni sabon salon siyasa ne, ban taba zuwa ba amma na aiwatar da dubban ayyuka, irin wadanda nake takara da su ba su yi kwata kwata.
Kwankwaso da Shekarau sun yi iya kokarinsu amma ni zan zo da wani abu na musamman.
Zaura ya ƙara da cewa, idan aka zabe mu, yin tunani a kan bukatunsu da aikinsu zai zama babban alhakinmu.
“Ba abin da zai hana ni ko ya tsorata ni in kasance tare da jama’ata, in taɓa rayuwar mutanena.
Babu wata barazana ko matsi da za ta raba ni da talakawa, al’umma ta.
Ina gare su kuma su nawa ne,” in ji shi.
Jigon na APC ya yi alkawarin yabawa kokarin gwamnatin jihar a fannonin kiwon lafiya, ilimi, tituna, noma, ababen more rayuwa, ci gaban bil Adama da dai sauransu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇