Bacin Rana! Dubun wani ƙasurgumin ɓarawon Awaki da ya addabi al’umma ta cika

📸Yan Sanda

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun kama wani da ake zargin ƙasurgumin ɓarawon akuyoyi ne da ya kware wajen satar awaki ta amfani da makamai a kauyen Pasali Konu da ke karamar hukumar Kagarko a jihar.

Alfijir Labarai ta rawaito Kakakin rundunar, Mansur Hassan, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai a yau Lahadi a Kaduna, cewa an kama wanda ake zargin ne a jiya Asabar.

ASP Hassan, ya ce a ranar 11 ga Nuwamba, da misalin karfe 4: 30, tawagar sa ido da ‘yan sintiri, a yayin da suke sintiri a kauyen, suka kama matashin mai shekaru 20 da haihuwa.

A cewarsa, wanda ake zargin ya fito ne daga kauyen Igwa na karamar hukumar Kagarko.

Ya bayyana cewa wanda ake zargin na ɗauke da muggan makamai da kuma hular rufe fuska.

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

“Wanda ake zargin, wanda ya kware wajen satar awaki, ya amsa cewa su biyu ne da suka zo kauyen domin satar awaki,” in ji Mista Hassan.

Ya ce da suka ga tawagar ‘yan sintiri, sai dayan da ake zargi da ya gudu, yayin da aka kama na biyun.

Kakakin ‘yan sandan ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu bayan kammala bincike na farko, inda ya ci alwashin kamo na biyun da ya tsere.

Daily Nigerian

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *