Bayan Bashi Sabon Adaidaita Da Daukar Nauyin karatunsa An Sake Gwangwaje Ɗan Sahu Da Ya Mayar Da Miliyan 15

Matashin mai baburin Adaidaita sahun nan da ya tsinci tsabar kudi miliyan goma sha biyar ya kuma dawo dasu ga masu shi,  ya rabauta da   kyautar kudi dubu 100 da Shaddoji, wanda Alhaji Mustapha Garba Dan Darman din Sokoto ya bashi.

Alfijir Labarai ta rawaito wani bawan Allah ya Gwnagwaje Auwalu Salihu da Sabon Adaidaita Sahu kyauta, duk wadannan tagomashi suna zuwa ne bayan halin kirki da ya nuna na mayar da makudan kudaden da ga tsinta, lokacin da ake cikin wani irin yanayi na kunchi da matsin rayuwa.

Sakamakon wannan abin kirki da yayi, Alhaji Bashir Gentile ya kai yaron gidan wani babban mai arziki a birnin Kano, inda ya bashi kyautar sabon baburin adaidata sahu, dana wanda yake amfani da shi na haya ne.

Kuma wannan attarijin yayi ummarni a mai da yaron makaranta, ya dauki nauyin karatunsa tun daga farko har karshe.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

One Reply to “Bayan Bashi Sabon Adaidaita Da Daukar Nauyin karatunsa An Sake Gwangwaje Ɗan Sahu Da Ya Mayar Da Miliyan 15”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *