Bayan Kashe Jami’in Bijilanti Yan Sanda Sun Cafke Mutumin Da Ake Zargi A Kano

FB IMG 1718878988386

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta samu nasarar cafke mutum daya daga cikin ƴan dabar da ake zargin sun kashe kwamandan ƙungiyar Bijilante na unguwar Ja’en dake jihar Kano, mai suna Muhktar Garba, wanda akafi sani da Baballiya.

Alfijir labarai ta ruwaito hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana.

Kiyawa ya ce bayan samun rahoton faruwar faɗan dabar a tsakanin ƴan unguwar Ja’en Maƙera, da kuma wasu ƴan unguwar Ja’en Ƴan Dillalai, ne aka tura jami’an ƴan sanda don su samar da tsaro a yankin.

“Daga rahotannin da muká samu faɗa ne na ƴan Daba, da ya kaure a tsakanin ƴan unguwar guda biyu a daren ranar Talata, inda ƴan dabar suka rufe kwamandan Bijilanten da sara da makamai har ta kai ga sun yi masa illa bayan an kai shi Asibiti ya rasu, “in ji Kiyawa”.

Ya kuma ce zuwa yanzu akwai wani mutum ɗaya daga cikin ƴan dabar da aka gane shi kuma yana hannun ƴan sanda a babban sashin binciken manyan laifuka ɓangaren kisan kai ana faɗaɗa bincike.

SP Kiyawa, ya ƙara da cewa rahotannin da suka samu daga jami’an su yanzu haka komai ya fara dai-dai ta ƙura ta lafa, inda mutane suke gudanar da al’amuran su na yau da kullum.

A daren Talata ne aka zargi wasu ƴan Daba daga unguwar Ja’en Maƙera, suka shiga unguwar Ja’en Ƴan Dillalai, inda suka haifar da faɗan Daban, lamarin da har suka kashe kwamandan Bijilanten na Ƴan Dillalai, wanda tuni akayi jana’izar sa a jiya Laraba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *