Bayan muggan hare-haren ‘Yan bindiga gwamnatin Kebbi ta raba kayan tallafi a Kebbi da Sokoto

Wadanda suka rasa matsugunansu sun nemi mafaka a kauyen Jarkuka da ke karamar hukumar Arewa ta Kebbi.

Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnatin jihar Kebbi, a ranar Litinin, ta raba kayan agaji ga wadanda hare-haren ‘yan bindiga suka rutsa da su daga kauyuka bakwai na jihohin Sokoto da Kebbi.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya bayyana cewa an kai hari kauyuka biyu a Kebbi da biyar a jihar Sokoto.

Wadanda suka rasa matsugunansu sun nemi mafaka a kauyen Jarkuka da ke karamar hukumar Arewa ta Kebbi.

Kwamishinan yada labarai da al’adu, Alhaji Yakubu Ahmed-BK ya ce kauyukan da lamarin ya shafa na kan iyakokin jihohin biyu.

“Muna wannan kauyen ne a madadin Mai Girma Gwamna Nasir Idris, domin raba kayan agaji ga wadanda hare-haren ‘yan bindiga suka raba da muhallansu.

“Gwamnan da ya samu labarin harin da aka kai a kewayen kauyukan da ke kan iyaka tsakanin jihar Kebbi da jihar Sokoto, sai ya fara aiki.

“Muna sane da halin da dubban ‘yan gudun hijira daga yankunan da aka kai hari suka shiga cikin wannan kauye da sauran kauyukan da ke kewaye domin tsira,” in ji Ahmed-BK.

Ya ce “kayan agajin sun hada da dubunnan buhunan gero, shinkafa da wake da kayan yaji da dai sauransu, a matsayin matakan gaggawa na rage radadin wadannan mutane.”

Ahmed-BK ya ce duk da cewa wadanda abin ya shafa ‘yan asalin jihar Sokoto ne, amma duk da haka, a matsayin gwamnati na jama’a da jama’a gwamnan ya ba da umarnin a yi wa duk wadanda abin ya shafa daidai da su.

Kwamishinan ya ce sun je kauyen ne domin tabbatar da rarraba kayayyakin agajin cikin adalci.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *