A cikin wata takarda mai cike da girgiza zuciya da kuma tonon silili da fallasa abubuwan boye, wadda ya aika wa Shugaban Nigeria Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Mai ritaya Babban Birgediya Janar Danjuma Ali-Keffi ya bayyana abin da ya kira wata mummunar kaddarar juya-hali da ya faru bayan wata babbar nasara da aka samu a yaki da ta’addanci a Najeriya.
A cewar wannan babban jami’i, bayan ya jagoranci ƙungiyar musamman ta soji wadda ta kama manyan shugabannin Boko Haram – ciki har da wanda ya kira “ainihin shugaban kungiyar” – maimakon a yaba masa, sai aka rama masa da mugunta: aka yi masa ritaya ta dole, tare da kama Shi, har tsawon kwanaki 64 a kurkuku shi kaɗai.
Ali-Keffi, wanda ya taba jagorantar Runduna ta 1 ta Sojan Najeriya a matsayin GOC, shi ne aka zaɓa kai tsaye don jagorantar “Operation Service Wide,” wata tawaga ta binciken yaƙi da ta’addanci da fadar shugaban kasa ta kafa.
Rahoto ya nuna cewa wannan aiki ya tona asirin ba wai shugabannin Boko Haram kaɗai ba, har ma da hanyoyin kuɗin da ke ɗaukar nauyin ta’addancin – ciki har da manyan jami’an gwamnati, hafsoshin soja, da manyan bankuna.
“Da zaran mun kama wasu daga cikin wadannan mutane muka fara fallasa hanyar kuɗin ta’addanci, sai farmaki ya dawo Kan mu,” in ji Ali-Keffi a wasikarsa.
Ya ce wasu manyan mutane masu ƙarfi a ciki da wajen gwamnati suna gaggawar kakkabe aikin tona asirin su da kuma toshe bakin duk mai ƙoƙarin fallasa gaskiyar.
Abin da ya kara girgiza jama’a shi ne yadda Janar ɗin ya nuna shakku game da mutuwar Lt. Gen. Ibrahim Attahiru, tsohon Shugaban Rundunar Sojojin Kasa, wanda ya mutu a hatsarin jirgi a 2021. A cewar Ali-Keffi, Attahiru marigayin Lt Gen. Ibrahim Attahiru ya kuduri aniyar kamo masu daukar nauyin ta’addanci, kuma ya amince da aikin Operation Service Wide.
Janar ɗin ya yi nuni da cewa watakila mutuwar Lt Gen. Ibrahim Attahiru ba ta kasance haɗari na gaskiya ba, ya kuma roki Shugaba Tinubu ya sake duba lamarin, tare da bude sahihin bincike na gaskiya kan hatsarin da kuma dukkan handama da ake yi wa yaki da ta’addanci.
Wadannan zarge-zarge da Ali-Keffi ya bayyana, yanzu sun haifar da kira ga bincike na gaskiya. Duk da cewa gwamnatin tarayya bata fitar da martani ba tukuna, maganganunsa suna da nauyin da ba za a yi watsi da su ba. Idan gaskiya ne, hakan na nuni da cewa akwai wasu gungun shaidanun bila’adama masu tsananin ɓarna da su ke dakile yaki da ta’addanci daga cikin tsarin gwamnati da kuma Cikin rundunar tsaro – inda jarumai masu aiki domin kare kasa ke samun mummunan hukunci maimakon yabo.
Fallasar Ali-Keffi ta buɗe sabon babi a cikin kalubalen tsaron Najeriya. Labarinsa yana tayar da hankula da samar da tambayoyi masu nauyi: wa ne yake cin moriyar tsawaita yaki da Boko Haram? Kuma me ya sa ake katsewa da Kuma toshe bakin wadanda ke yaki da ta’addanci daga cikin tsarin gwamnati?
Har sai an amsa wadannan tambayoyi da gaskiya da jarumtaka, yaki da ta’addanci a Najeriya zai ci gaba da samun cikas – ba saboda rashin dabarun yaƙi ba, sai dai saboda cin amana daga cikin manyan jagororin Siyasa masu mulki da Suka game bakin su da mukiyan Nigeria na kashashen waje.
“Akwai zargi mai ƙarfi cewa CIA ta Amurka tare da haɗin gwiwar gwamnatin Najeriya a lokacin Shugaba Obasanjo, kuma da sanin Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), su ne suka tsara kafa Boko Haram.
Har ila yau, ana danganta cewa bayan rasuwar Umar Musa Yar’Adua, Shugaba Goodluck Jonathan ya ci gaba da wannan mummunan shiri.
Bisa ga wannan zargi, manufar ita ce a raunana Musulmi a Najeriya ta hanyar rage yawan su – domin an tabbatar cewa tara cikin goma na wadanda Boko Haram ta kashe ko ta cutar, Musulmai ne.”
Ibrahim Muhammad Dantata/ Mikiya Hausa
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t.