
Alfijr ta rawaito Jam’iyyar APC a jihar Kano ta yi kira ga mambobinta da magoya bayanta da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka da oda biyo bayan sake duba sakamakon zaben ranar 18 ga watan Maris, na zaben gwamna da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ke yi a halin yanzu.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Talata.
Idan zaku tuna cewa, bayan ayyana dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP, Abba Kabiru Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben da INEC ta yi, jam’iyyar APC ta rubuta wasikar zanga-zangar neman a sake duba sakamakon zaben tare da bada wa’adin kwanaki bakwai.

Duk da dai har yanzu INEC ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan bukatun jam’iyyar APC ba.
Sanarwar Garba ta ce jam’iyyar za ta yi duk mai yiwuwa a cikin tanade-tanaden doka da sauran hanyoyin da aka shimfida domin ganin an yi adalci a lamarin.
Sanarwar ta bayyana cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da mataimakinsa dan takarar gwamna, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da mataimakinsa Murtala Sule Garo sun bayyana gamsuwarsu da yadda ‘ya’yan jam’iyyar ke gudanar da rayuwarsu kafin zabe
da kuma bayan zabe.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇