Cikin Girmamawa Tare Da Ladabi Da Biyayya Muke Amfani Da Wannan Damar Domin Aiko Maka Sakonmu Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusif
A Matsayinmu Na Tsofaffun Dalilan Wannan Makaranta Kuma Yan Wannan Unguwa Muke Sanar Da Kai Halin Da Wannan Makaranta Take Ciki Bayan Rushe Shagunan Da Aka Yi, Musamman Ta Kan Titin IBB Kasuwar Kwari.
A yanzu Wannan Makaranta Ta Kasance Bata Da Tsaro Duba Da Yan daba da bata gari suke shiga Suna cin karensu babu babbaka sakamakon makarantar ta zama budaddiya, duk sanda mutum yaga damar shiga zai shiga
.

Ya mai girma Gwamna ga Ire-Iren abubuwan da suke faruwa a ciki;
-Shaye-Shayen Miyagun Kwayoyi.
Matasa Nashiga Suyi Bayan Gida (KASHI) Da Fitsari Har Aciki Da WajanAzuzuwa.
-Satar Kofofi Da Tagogin Makaranta
-Satar Duk Wani Abinda Yake Da Daraja A Cikin Makarantar.
Hakazalika Mai Girma Gwamna Kasa Da Kwana Goma Bangaren Gwaje-Gwaje Na Kimiyya (BiologyLaboratory)Ya Kama Da Wuta, Kuma A Bisa Bincikenmu Hakan Na Da Nasaba Da Wutar Taba Wiwi Da Sigari Da Yan Shaye-shaye Suke Yi A cikin Makarantar.
Muna Kyautata Zaton Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf Bai San Hakan Ba Kuma Zaiyi Abinda Ya kamata Domin Daukar Matakin Gaggawa Kafin Dalibai Su Dawo Daga Hutu.
Mun Rasa Yadda Zamu Sami Ganinka Ko Tura Maka Sako! Shi Yasa Muka Yi Amfani Da Jaridar Alfijir Labarai Domin Mun San Sakon Zai Isa Gareka.





Sa Hannun :Umar Aminu Umar Shuagaban Dalibai Na Shekarar 2017.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl