Budaddiyar Wasika Daga Jaafar Jaafar Zuwa Ga Gwamna Abba Kabir Yusif

FB IMG 1709295932803

Tun da gwamna bai ba wa na kusa da shi dama ko fuska su ba shi shawara ba, to kuwa lallai haƙƙi ya rataya a kan duk mai kishin Kano ya faɗa masa gaskiya.

Mai girma Gwaman Kano Abba K. Yusuf sai ka gyara mu’amillar ka da mashawartanka da kuma masu riƙe da muƙaman gwamnati.

Zancen da mu ke ji shi ne kwamishina sai ya yi wata da watanni ya na son ganin gwamna kan abu mai muhimmanci amma ya kasa gani ko magana da gwamna ta waya. Wannan bai kamata ba, domin kuwa hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka.

Binkicen da na yi ya nuna cewa Mallam Daurawa ya yi yunƙurin ganin gwamna don tattaunawa da shi kan matsalar Murja Kunya amma gwamna bai ba shi dama ba. Ya yi yunƙurin yi masa bayani ta waya, nan ma abin ya ci tura.

Sukar da gwamna ya yi wa Hukumar Hisba jiya a bainar jama’a kamar mutum ne ya daɓa wa kansa wuka, domin kuwa gwamnatinsa ya zaga. Kuma dole jama’a su ce saboda Hisba ta kama Murja Kunya gwamna ya yi wannan magana — domin kuwa a lokacin da Hisba ta ke kama masu baɗala ta na jefa su a bayan mota gwamna bai ce uffan ba sai bayan an kama wannan yarinya.

Duk mai hankali ya san cewa akwai hannun gwamna (ba wani gwamnati, GWAMNA) dumu-dumu a fitar da murja daga gidan yari ba bisa doron doka ba. ‘Yan watannin baya kamar mu haukace saboda ana yunƙurin kawar da gwamnatinka ba bisa doron doka ba, amma abin takaici kai kuma ka yi wa doka hawan ƙawara saboda wata ballagaza bankaura.

The recipe for losing popularity as a leader is putting your interest on collision course with public interest. Governor Yusuf should not take this for granted.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

One Reply to “Budaddiyar Wasika Daga Jaafar Jaafar Zuwa Ga Gwamna Abba Kabir Yusif”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *