Budaddiyar Wasika Daga Sheikh Kabiru Gombe Zuwa Ga Shugaban Kasa Tinubu

FB IMG 1709542414023

Sheikh Kabir Muhammad Haruna Gombe ya yi kira ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta duba halin da mafi yawan mutane suka shiga

Malamin wanda shugaba ne a kungiyar Izala ya ce ana yunwa a kusan ko ina, kyau a bude baitul-mali domin a taimakawa Bayin Allah, Kabir Gombe bai ga amfanin a tara kudi da nufin yin ayyukan more rayuwa ba, alhali wadanda ake mulka suna neman mutuwa da yunwa.

Kabiru Gombe ya ba gwamnati shawarar ta raba abinci domin a samu saukin yunwa da talauci da ya yi katutu a ko ina.

“Wallahi, al’umma tana cikin masifa da talauci da yunwa, duk wanda ya fada maka babu wannan, abin bai iso gidansu ba ne.”

“Da wannan mu ke kira ga shugaban kasar Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.” mutane suna cikin yunwa. Babu lokacin da ya kamata gwamnati ta taimaki alum a kamar irin wannan lokaci.”

Mai girma shugaban kasa a bude baitul-malin gwamnati, a debi dukiya a saye abinci, idan akwai abincin a ajiye, a fito da shi.
A sayo abinci a taimakawa talaka. Mun san kuna da burin nan gaba ku yi hanyoyi, idan yunwa ta kashe talaka kafin ranar da za ayi hanyar, menene amfaninta a wajensa?”

Malamin ya ce idan aka raba tireloli na shinkafa, masara, gero, dawa, taliya, sukari da garin tuwo, gwamnatin nan za ta samu albarka.

Sakataren na kungiyar Izala ya kara da cewa za a dauki shekaru masu yawa ana tunawa da Bola Tinubu idan ya saukakawa talaka. Akwai sauran kasashen duniya da ba su kai Najeriya yawan arziki ba su ke rayuwa a sauki.

Babu amfanin tara kudi da ake yi bayan cire Tallafin Mai, domin za a iya Samun yan handama su wawashe.

A karshe ya yi kira ga masu hali da wadata su rika taimakawa marasa shi, domin rowa Zata kara jefa kasar a cikin karin bala’i.

News NG

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *