Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Mai Girma Jagora Kwankwaso Da Gwamnan Kano Abba Kabir

Kwankwasiyya

Kukan Zuciya Akan Sakin Sunan Dan Takarar Kansila na Mazabar Kwachiri

Ina rubuto wannan wasika ne domin sanar da ku game da matsalar da ta taso dangane da sakin sunan dan takarar kansila na mazabar kwachiri a Karamar Hukumar Fagge.

Kamar yadda kuka sani, na sayi (Form) domin tsayawa takarar kujerar Shugaban Karamar Hukumar Fagge. Duk da haka, a lokacin da shugabana jagoranmu, SanataRabi’u Musa Kwankwaso, ya umarce mu da mu nemi maslaha a lokacin taro, na bi umarninsa ba tare da jinkiri ba, na kuma janye daga takarar.

Wannan mataki ya ba da mamaki ga jagoranmu, in da ya umarci shugabannin jam’iyya da su saka sunayen mu wadanda muka janye a gaban jagora mai girma Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin”yan takarkaru na kansiloli na mazabar da mutum ya fito.

Ni kuma naga ya dace da a bani Mazabar kwachiri tunda daga nan na fito.

Amma duk da wannan umarni daga shugabanmu, ba a tuntube ni ba, kuma abin mamaki, wani mutum wanda bai janye daga takara ba, aka fitar da sunansa a matsayin dan takarar kansila ba tare da sanina ko amincewa ba, wanda ya saba da umarnin da shugabanmu Maigirma Eng. Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayar.

A saboda haka, nake kai kukana ga jagoranmu Eng Rabiu Musa Kwankwaso da kuma Gwamnan Kano kan yadda wannan lamarin ya
gudana.

Ina neman da a sake duba batun, a kuma girmama umarnin shugabana na sanya ni a matsayin dan takarar kansilan Kwachiri Ward kamar yadda aka umarci da ayi

Ina fatan za a bawa wannan batu muhimmanci, kuma ina fatan samun mafita mai kyau.

Na gode da lokaci da kulawar ku.
Naku mai biyayyarda da girmamawa a gareku.

Abdullahi Dahiru Muhammad (Maikano)
Dan Jam’iyya, NNPP Mazabar Kwachiri, Karamar Hukumar Fagge

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

One Reply to “Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Mai Girma Jagora Kwankwaso Da Gwamnan Kano Abba Kabir”

  1. Assala’alaikum
    Best Seller
    Aganina wannan shine abunda ya faru a mafi yawancin mazubu, misali a maza6ata ta Yanoko, muna da yan Takara mutum 11, Amma sai mukaji wai wasu mutum 2 ne suka za6i wanda zai wa jam’iyyar NNPP Takara ba tare da tuntu6ar Sauran yan Takarar ba.
    Haka ta kasance ga dan takarar Shugabancin Karamar Hukumar Tofa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *