Cikakken Bayanin Atiku kan sakamakon Kotun Koli daya gabata

FB IMG 1696527773380

Ya Kamata Najeriya Ta Fara Tsarin Mulki Na Shekara 6, Babu Tazarce

Alfijir Labarai ta rawaito tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya bayar da shawarar a rika kammala dukkan shari’un zabe kafin a kai ga rantsar da wanda ya lashe shi.

Ya kuma ce hukuncin Kotun Koli kan nasarar Shugaba Bola Tinubu na makon da ya gabata, ya bar baya da kura matuka.

Atiku dai ya tsaya kai da fata cewa sam Tinubu bai ma cancanci ya tsaya takarar shugaban ba a zaɓen da ya gabata.

Dan takarar ya kuma zargi Kotun Kolin da kuma Hukumar Zabe ta Kasa da goyon bayan rashin gaskiya, damfara da kuma ɗaure wa ƙarya gindi.

A makon da ya gabata ne dai Kotun Kolin ta tabbatar da nasarar da Tinubu ya samu a zaben sannan ta yi watsi da ƙarar da Atiku da takwaransa na LP, Peter Obi suka shigar a gabanta suna kalubalantar nasarar.

Hakazalika Atiku ya bayar da shawarar fara amfani da wa’adin shekara shida a kujerar Shugaban Kasa kuma babu neman tazarce.

Hakan, a cewarsa, zai rage neman sake lashe zabe ko ta halin ƙaƙa ga masu rike da kujerar.

Ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai na kasa da kasa da ya kira a Babban Birnin Tarayya Abuja a ranar Litinin.

Dogaro da sakamakon binciken da ya yi a kan takardun karatun Tinubu a Jami’ar Jihar Chicago (CSU) da ke Amurka ne ya saka ya garzaya gaban kuliya, amma kotun ta ce ba ta da hurumin sake karbar sabuwar shaidar da ba a gabatar a kotunan kasa ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *