Alfijr
Alfijr ta rawaito Akalla yara 77 ne aka ceto daga wani gida da ke karkashin kasa a wani coci a garin Ondo na jihar Ondo.
Majiyar ta tattaro cewa an sace yaran ne aka ajiye su a dakunan karkashin kasa.
Jami’an tsaro na ‘yan sanda a garin sun kama limamin cocin da sauran masu hannu da shuni.
Alfijr
An ga yaran da aka sace a wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ne, an gan su a cikin motar ‘yan sanda da ke sintiri wadda ta kai su ofishin ‘yan sanda.
An ji wata murya a cikin faifan bidiyon tana cewa “Akwai yaran da aka yi garkuwa da su a cikin dakin karkashin kasa na wani coci a Unguwar Valentino a Ondo.
Alfijr
“An kama Fasto da wasu ‘yan cocin kuma suna cikin motar ‘yan sanda da ke sintiri.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Funmi Odunlami, ta tabbatar da gano lamarin da jami’an ‘yan sandan suka yi.
Odunlam ya ce an kai wadanda harin ya rutsa da su hedikwatar rundunar ta Akure.
Alfijr
A cewarta, “Bani da cikakken bayani tukuna amma suna kawo wadanda abin ya shafa hedikwatar. “Zan baku cikakken bayani da zarar na samu daga DPO.”