Alfijr
Alfijr ta rawaito Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya dakatar da Sarkin Birnin Ƴandoto, Aliyu Marafa, bisa bada sarautar Sarkin Fulani ga wani ƙasurgumin shugaban ƴan fashin daji da ake nema ruwa a jallo, wato Adamu Aliero-Yankuzo, wanda aka fi sani da Ado Alero.
Matakin da Masarautar ta dauka ya jawo bacin rai, inda jama’a da dama suka yi Allah-wadai da irin karramawar da aka yi ga wannan kasurgumin ɗan ta addan.
Alfijr
Wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Kabiru Balarabe ya fitar, gwamnatin ta barranta kanta daga matakin na Sarkin ya dauka, inda ta dakatar da shi, tare da kafa kwamitin da zai binciki lamarin.
Kuma gwamnatin ta bada rikon sarautar ga Alhaji Mahe Garba Marafa, Hakimin Ƴandoto.
Sai dai kuma masarautar Ƴandoton ta ce ta ɗauki matakin naɗin sarautar ne domin kawo zaman lafiya a ya kin na Tsafe da maƙwabtan yankin.
Alfijr
A jiya Lahadi ne dai Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa cincirindon al’umma ne su ka halarci bikin naɗin sarautar da Sarkin ya yi wa Ado Aliero, duk kuwa da cewa a shekaru biyu da su ka gabatar rundunar ƴan sanda ta sanya ladan Naira miliyan 5 ga duk wanda ya gano inda ya ke.
Wato shi Ado Aliero, shine babban ɗan fashin dajin da ya addabi jihohin Zamfara da Katsina.