Da Ɗumi Ɗuminsa! Gwamnatin Jihar Kano Ta Haramta Amfani Da Adaidaita Sahu Bayan Karfe 10:00 Na Dare

Alfijr

Alfijr ta rawaito Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da dakatar da zirga-zirgar babura masu kafa uku da aka fi sani da A Daidata Sahu daga karfe 10:00 na dare zuwa 6:00 na safe daga ranar Alhamis 21 ga Yuli, 2022.

Sanarwar da ya fitar Kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba ya nuna cewa an cimma matsaya kan hakan ne a karshen taron tsaro na jihar.

Alfijr

Ya ce matakin wani bangare ne na kokarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar. Kwamishinan, a cikin sanarwar, ya bukaci masu tuka keke masu kafa uku da su bi su kuma daina aiki a cikin sa’o’in da aka kayyade domin jami’an tsaro za su aiwatar da dokar ba tare da yin sulhu ba.

MALAM MUHAMMAD GARBA Hon. Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano