Da Ɗumi Ɗuminsa! Wasu Mutane Sun Dambace A Gaban Masallacin Ka’aba

Alfijr ta rawaito Rikici ya ɓarke a gaban Masallacin Ka’aba na Kasar Saudiyya yayin gudanar da aikin Umrah

Jami’an tsaro na musamman da ke kula da aikin Hajji da Umrah a Saudiyya sun ƙaddamar da bincike kan faɗan da ya ɓarke tsakanin wasu mutane biyu a yankin Al-Mas’a da ke cikin Masallacin Harami na Makkah a ranar Alhamis.

Ba a samu rahoton wani rauni ba sakamakon faɗan da suka yi amma an ɗauki matakai game da mutanen biyu, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.

Jami’an tsaron da ke aikin kula da Hajji da Umrah sun yi kira ga masu ibadah da su mutunta alfarmar Ka’aba da kuma kiyayewa tare da kasancewa cikin natsuwa yayin gudanar da aikin ibadar umrah da sauran ibadu a Masallatai biyu masu alfarma a Saudiyya.

Alfijr

Kamar yadda BBC Hausa suka wallafa