Wani Gini Ya Ruguje A Kano, Ya Kashe Mutane Biyu, Mutum 3 Na Halin Mutu ‘Kwa ‘ kwai

Alfijr

Alfijr ta rawaito wani gini da bai kammala ba a Kano ya ruguje da tsakar dare a cikin birnin Kano, ya yi sanadin mutuwar mutane 2 tare da raunata wasu mutane 3.

Tsautsayi ya faru ne a unguwar Hotoro Gabas bayan gidan Man Chula, da misalin karfe 3 na daren Juma’a.

Wani ganau ya shaida wa wakilin jaridar Nigerian Tracker da ya ziyarci wurin da lamarin ya faru cewa ginin da ba a kammala ba yana kusa da makarantar Al-Qur’ani ta gargajiya inda daliban makarantar 5 ke ciki da barci A daren ranar, 2 daga cikin daliban biyar din sun rasu yayin da sauran 3 ke fama da raunika.

Alfijr

Daliban da suka rasu su ne Ali mai shekaru 28 da kuma Abdulganiyu mai shekaru 22.

Tuni dai aka yi jana’izarsu a safiyar ranar Asabar.

Wasu shaidun gani da ido sun kuma shaidawa Nigerian Tracker cewa ginin bai yi kyau ba saboda ana samun matsalolin da ke tattare da tsarinsa da kuma buladin da da ake amfani da su.

Alfijr

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto har yanzu mai gidan bai bayyana ba.

Slide Up
x