
Alfijr ta rawaito kulof din ƙasar Saudi Arabiya, Al-Hilal, yana neman siyan Cristiano Ronaldo.
Ronaldo yanzu ya zama dan wasa bayan Manchester United ta soke kwantiraginsa a wannan makon, bayan hirar da ya yi da Piers Morgan.
A cikin hirar, dan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar ya soki kungiyar da masu shi da kuma kocinta Erik ten Hag.
Dan wasan mai shekaru 37 a halin yanzu yana gasar cin kofin duniya tare da Portugal kuma ya zura kwallo a raga a wasansu na rukuni da Ghana ranar Laraba.
United ta samu tayin siyan Ronaldo daga Saudi Arabiya a bazara, amma daga karshe yarjejeniyar ta ci tura.
A cikin hirar da yayi da TalkTV, Ronaldo ya yi ikirarin cewa ya ki daukar matakin, wanda ya kai kusan fam miliyan 305.
Sky Sports ta ce idan Al-Hilal ta sayi Ronaldo, za su saurari tayin Odion Ighalo, wanda kwantiraginsa ya kare.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ