Da Ɗumi Ɗumin! Kungiyar NLC da TUC sun sanar da fara yajin aikin gama gari

Screenshot 20231103 172349 com.android.chrome edit 94247829761139

Kungiyoyin kwadagon da suka hada da Najeriya Labour Congress da Trade Union Congress of Nigeria sun bayyana shirin shiga yajin aikin a fadin kasar, sakamakon ragargaza da kuma sace shugabansu Joe Ajaero.

Alfijir Labarai ta rawaito yajin aikin da aka shirya gudanarwa a ranar Laraba 8 ga Nuwamba, 2023, wanda aka bayyana shi ne a wata ganawa da manema labarai a ranar Juma’a 3 ga Nuwamba, 2023.

A cewar shugabannin kungiyar ta hadin guiwa, an baiwa gwamnatin tarayya bukatar wasu abubuwa shida da suka hada da a gaggauta tsige kwamishinan ‘yan sanda, jihar Imo da kwamandan yankin, da sauran jami’ai, bisa zarginsu da hannu wajen cin zarafi da wulakanci ga Ajaero da sauran ma’aikata.

Idan Zaku iya tunawa cewa shugaban NLC ya je Owerri a ranar Laraba 1 ga Nuwamba, 2023, don tara ma’aikatan Imo don gudanar da zanga-zanga a jihar bisa zargin cin zarafi da cin zarafin ma’aikata da gwamnatin jihar ta yi.

A yayin wannan zanga-zangar an yi taho-mu-gama wanda ya kai ga raunuta Kwamared Ajaero, wanda yanzu haka an ce an kai shi kasar waje domin samun ingantacciyar lafiya.

Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta musanta kama shugaban kungiyar.

Gwamnan Imo ya kuma musanta cewa yana da hannu a balajirar da Ajaero ya fuskanta, kuma ya zarge shi da yin katsalandan a harkokin siyasar jihar.

Uzodimma ya yi wannan zargin ne a ranar Alhamis bayan karbar tutar jam’iyyar APC daga hannun shugaba Bola Tinubu a fadar Aso Rock Villa da ke Abuja.

“Shugaban NLC na kasa dan jihar Imo ne kuma bai iya tantance banbancin zama shugaban kungiya na kasa ba, sannan kuma mai sha’awar siyasar cikin gida,” in ji Uzodimma.

Ajaero, yayin ganawa da manema labarai a farkon makon, ya zargi gwamnatin jihar Imo da “tauye hakkin ma’aikatan Najeriya a jihar,” don haka ya sha alwashin hada kan ‘ya’yan kungiyar a jihar don gudanar da yajin aikin gaba daya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *