An Sace Dan Dokta Zahra u Kwamishiniyar Mata Da Walwala A Kano

Dr Zahra u da iyalansa suna cikin fargaba damuwa da rashin sanin halin da dansu Abdurrahman yake ciki.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa Abdurrahman ya bar gida tun a ranar 17 ga watan Janairun 2022, zuwa jihar Katsina inda yake hidimar kasa a can.

Tun daga lokaci ba a sake jin duriyarsa ba, an yi kokarin nemana a Waya shiru ba a same shi ba.

Iyalan Kwamishiniyar sun je don nemansa a Katsina, amma aka ce musu bai je can din ba.

Har ya zuwa yanzu babu wata hujja da za a iya cewa sace Abdurrahman aka yi kamar yadda majiyar ta bayyana.

Majiyar ta bayyana cewa ba a sami wani kira daga wasu mutane ba akan neman kudin fansa ko wani abu makamancin hakan.

Kwamishiniyar, Dokta Zahra’u ta ce kimanin kwana 11 ke nan babu labarin in da dan nata yake.

Za a iya cewa batun batan mutane a Jihar Kano yana kara yawa a ’yan watannin nan, jami’an tsaro a Jihar Kano suna nan suna aiki don gano wurin da Abdurrahman yake.

Slide Up
x