Mai shari’a Abiola Soladoye na kotun laifuka na musamman a jihar Lagos, Ikeja, ya yanke wanda ake zargin mai suna Sunday Oyedele hukuncin daurin rai da rai a kan laifin lalata ‘yar makwabcinsa ‘yar shekara uku.
An gurfanar da Oyedele a gaban kotu a ranar 29 ga Afrilu, 2019, a kan laifin lalata karamar Yarinya, a unguwar Itamaga da ke Ikorodu, jihar Lagos.
Punch ta rawaito mai gabatar da kara, Oyedele ya aikata laifin ne a watan Nuwambar 2017.
Lokacin shari’ar, masu gabatar da kara sun gabatar da shaidu hudu, ciki har da wani likita daga cibiyar kula da lalata da mata ta Mirabel Centre, Dokta Oyedeji Alagbe.
Alagbe, a cikin shaidarsa, ya ce binciken likita ya nuna cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya yi lalata da yarinyar ta dubura da kuma ta farji.
Da take yanke hukuncin a ranar Talata, Mai shari’a Soladoye ta ce masu gabatar da kara sun tabbatar da tuhumar da ake yi na lalata da su ba tare da wata shakka ba.
Mai shari’a ta ce, “Sabo da ƙazantar, abin takaici ne; wanda ake tuhuma kazamine kuma azzali ɗan jari hujja, wanda yakamata a kulle shi.
An tabbatar da tuhume-tuhumen da ake tuhumar wanda ake tuhuma ba tare da wata shakka ba. “Wanda ake tuhumar, bayan an same shi da laifi, an yanke masa hukuncin daurin rai da rai ba tare da zabin tara ba. Haka kuma za a yi masa rajista a rajistar masu laifin Fyade kamar yadda gwamnatin jihar Lagos ta tanada.”