Gwamnatin jihar Kano ta amince da ranar Lahadi, 15 ga Satumba, 2024, a matsayin sabuwar ranar da ɗaliban makarantun firamari da sakandire za su koma karatu domin fara zangon farko na shekarar 2024/2025 ga dukkan makarantun kwana a jihar.
Dalibain sauran makarantu na jeka ka dawo kuwa za su koma ranar Litinin 16 ga Satumba, 2024.
A wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar, Balarabe Abdullahi Kiru ya sanya wa hannu, kwamishinan ya bukaci iyaye da su tabbatar da cewa ya’yansu sun koma makarantunsu a ranar da aka ambata domin a ranar za su ci gaba da aiki domin tabbatar da cikakken bin doka.
Haka kuma ya shawarci dalibai da su guji shiga makarantunsu da duk wani abu da ya sabawa doka, kamar wukake ko reza, da dai sauransu.
Sanarwar ta sake jaddada kudurin gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusif na ganin kowane yaro ya samu ilimi mai inganci.
“Gwamnati na daukar matakai masu kyau wajen samar da ingantaccen yanayi na koyo da zai zaburar da karfafawa daliban mu kwarin gwiwa a fannin ilimi,” in ji sanarwar.
Sai dai sanarwar ta bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da bai wa ma’aikatar hadin gwiwa, tare da ba su tabbacin cewa gwamnati na daukar dukkanin matakan da suka dace domin tabbatar da ingantaccen yanayin koyo da koyarwa.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj