Da Dumi Duminsa! Hukumar NUC Zata Tantance Ingancin Ma’aikatan ilimi a matakin farfesa a kasar nan

Hukumar kula da jami’o’i ta kasa ta bayyana adadin manyan malaman jami’o’in Najeriya a kasa.

Best Seller Channel 

 Best Seller Channel 

A cewar NUC, yanke shawarar kimanta ingancin ma’aikatan ilimi a matakin farfesa shine saboda ana ɗaukar matakin farfesa a matsayin mafi girman ingancin ilimi. 

Hakan ya zo ne kamar yadda hukumar ta bayyana cewa jami’o’i 107 ne aka amince da su gudanar da karatun digiri na biyu. 

Hukumar ta NUC ta bayyana hakan ne a jerin bayanai da ta wallafa a shafinta na yanar gizo. 

Best Seller Channel 

Jaridar PUNCH a nazarin da tayi ranar Laraba tace, “Wannan shine tantance ingancin ma’aikatan ilimi a jami’o in. 

An zaɓi cikakken nau’in farfesa ne saboda shine mafi girman ingancin ma’aikatan ilimi a jami’a, “in ji NUC. 

Bayanai sun nuna cewa cibiyar da ta fi kowacce yawan malaman jami’a ita ce Jami’ar Usman Dan Fodio wadda ta samu kashi 36.44 bisa dari.

 Jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife, ta bi ta da kaso 35.80 cikin 100. 

Best Seller Channel 

Jami’ar Ibadan ta zo ta uku da kashi 29.04, yayin da Jami’ar Lagos ta zo a mataki na 16 da kashi 14.75 kacal na malaman jami’a. 

Sauran jami’o’in gwamnatin tarayya da ke da karancin farfesoshi su ne Jami’ar Tarayya, Oye Ekiti; Jami’ar Tarayya, Lafiya; Jami’ar Aikin Gona, Makurdi; da Jami’ar Uyo da dai sauransu. 

Ga jami’o’in mallakar jihohi, NUC ta lura cewa 11 daga cikinsu suna da kasa da kashi 10 cikin 100 na manyan malamai. 

Ya sanyawa cibiyoyin sunan Jami’ar Fasaha ta Cross Rivers, Jami’ar Jihar Kwara, Jami’ar Kiwon Lafiya ta Jihar Bayelsa, Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Jami’ar Jihar Adamawa, Jami’ar Fasaha, Jami’ar Maitama Sule, Jami’ar Jihar Bauchi, Jami’ar Jihar Gombe, da Jami’ar Jihar Kano, Jami’ar Kimiyya da Fasaha, da kuma Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi.

 A cikin rukunin jami’o’i masu zaman kansu, NUC ta lura cewa wasu cibiyoyi suna da ƙasa da kashi shida cikin ɗari na ƙwararrun malamai. 

Best Seller Channel 

Musamman Jami’ar Bowen, Jami’ar Baze, Jami’ar Summit, Jami’ar Crescent, Jami’ar Hallmark, Jami’ar Clifford, Jami’ar Igbinedion, Jami’ar Augustine, Jami’ar Al-Qalam, Jami’ar Landmark da Jami’ar Chrisland, da sauransu.

Slide Up
x