Da Dumi Duminsa! Wani Sabon Ma aikaci Car Wash Ya Shiga Hannu. Bayan Da Ya Sace Wata Sabuwar Mota

 HUKUMAR YAN SANDAN JIHAR KANO TA KAMA WANI  BARAWON SABUWAR MOTA A KANO. 

Best Seller Channel 

Best Seller Channel 

 DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanar da manema labarai a ranar Laraba Cewar,  a ranar 30/11/2021  wata Mata ta kawo rahoto daga wani mazaunin unguwar Badawa Quarters cewar an dauki Motar ta, Honda Accord 2017 Model, an dauke motar ne a wani Carwash dake Maidile Quarters, Kumbotso LGA, Jihar Kano. 

Best Seller Channel 

DSP Kiyawa ya ce, da samun rahoton kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi, ya umurci tawagar ‘Operation Puff Adder’ karkashin jagorancin CSP Alabi Lateef da su kwato motar tare da damke mai laifin. 

Best Seller Channel ta rawaito bincike na farko, an gayyaci mai Carwash, nan ya tabbatar wa rundunar Yan sandar cewa ya dauki wani Abdullahi, a matsayin ma’aikacin tsaftacewa a Cibiyar Carwash ba tare da sanin ko wanene shi ba. 

Best Seller Channel 

Ya Kara da cewar ya bar shi shi kadai bisa dogaro a Carwash inda ya dauko wannan motar. 

 A bisa bincike na gaskiya, an kama wanda ake zargin Abdullahi Sabo, mai shekaru 30, dan karamar hukumar Daura, jihar Katsina a garin Daura da motar sata. 

Wanda ake zargin ya amsa laifin satar Motar ne a  Carwash dake Kano inda aka dauke shi aiki, ya tafi da motar ne da niyyar sayar da ita . 

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi, ya kara gargadin cewa, masu aikata laifuka ba za su samu mafaka a jihar Kano ba. 

 In ba haka ba, za a kama su kuma su fuskanci fushin Doka. 

CP iDikko ya kuma godewa al’ummar Jihar Kano bisa addu’o’i da karfafa gwiwa da goyon baya da hadin kai, ya kuma bukaci mazauna yankin da su yi wa Jiha da kasa addu’a tare da kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su kuma kada su dauki doka a hannunsu. 

Best Seller Channel 

Wannan Sanarwa DSP ABDULLAHI HARUNA KIYAWA, ANIPR.

 Jami’in Hulda da Jama’a na ’Yan sanda, GA:- Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano ya fitar da ita. 

Slide Up
x