Da Dumi Duminsa! Wata Kotu Ta Iza Keyar Jaruma Mai ‘Kayan Mata’ Gidan Gyaran Hali Da Tarbiyya

 Kotu Ta Aike Da Jaruma Mai ‘Kayan Mata’ Gidan Gyaran Hali 

Best Seller Channel 

Best Seller Channel 

 Babban kotun Majistiri dake Birnin Tarayya Abuja ta aike da Jaruma wadda aka fi sani da  Hauwa Muhd  gidan gyaran hali.

 ’Yan sanda masu shigar da kara sun zargeta ne da ya da labaran karya, barazana da kuma bata suna.

Jaridar Aminiya ta rawaito, mai Shari’a, Ismaila Abdullahi l, ya sanya ranar Juma’a don yanke hukunci akan abinda ta shuka, ya kuma dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 23 ga watan Fabrairun 2022, inda ya ba da umarnin a garkameta a gidan gyaran hali da Tarbiyya na garin Suleja. 

Best Seller Channel 

Lauyoyi masu shigar da kara, E. A Inegbenoise da Chinedu Ogada, sun shaida wa kotun cewa wanda yake korafin, Ned Nwoko, ya kai karar Jaruma ta hanyar wani korafi da ta aike a rubuce ga ofishin ’yan sanda na Abuja ranar 20 ga watan Janairu don yin bincike a kai.

Inegbenoise ya ce Jaruma ta yi amfani da kafafen sada zumunta da dama, musamman shafinta na Instagram wajen wallafa bayanan karya a Ned Nwoko da matarsa, Regina, ya kuma yi ikirarin cewa Jaruma ta yi amfani da shafin nata na Instagram wajen cewa ta ba Regina Daniels din kwangilar Naira miliyan 10 don ta tallata mata kayan matan.

Best Seller Channel 

Lauyan ya kuma ce Jarima ta yi zargin cewa mai kara da matarsa sun karbi kudin nata amma suka ki tallata mata haja, a kwangilar da ba a taba ma kullata ba.

Lauyan ya shaida wa kotun cewa laifin ya saba da tanade-tanaden sassa na 392, 393, 397 da na 418 na kundin final kod.

Jaruma a na ta batun ta musanta laifukan da ake zarginta da su.

Slide Up
x