Dalibai Sun Babbake Gidan Shugaban Kwalejin Kimiyya A Birnin Kebbi

Kebbi

Daliban kwalejin kimiyya da fasaha ta Jega da ke jihar Kebbi sun kona gida da motar Shugaban kwalejin kimiyya da ke Jega, Haruna Sa’idu Sauwa, biyo bayan wasu zarge-zargen da suka yi da su.

Alfijir labarai ta rawaito Ɗaliban, sun yi zargin cewa, hukumar gudanarwar kwalejin ta karbo Naira miliyan 23 daga hannun dalibai dangane da rajistar dalibai 250 da suka yaye.

A cewar wata majiya mai tushe a cikin kwalejin, takaddamar ta samo asali ne daga wani sabon shirin kula da lafiyar al’umma da aka bullo da shi, wanda tun da farko ke da alaka da kiwon lafiyar da kuma kungiyar kula da lafiyar al’umma ta Najeriya.

Ya ce, daliban sun yi zargin akwai kunbiya kunbiya wajen karbar kudi, don haka suka yanke shawarar mayar da martani a wannan shigar tare da farfasa motoci da kona gidan shugaban, yayinda ma’aikatan kwalejin kowa yayi ta kansa kafin jami’an tsaro su kawo dauki.

Shugaban kwalejin wanda ya zanta da gidan rediyon Najeriya a wayar tarho ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya yi zargin cewa wasu ne daga wajen kwaleljin ki zuzuta wutar wannan rikicin ta amfani da daliban.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, SP Nafiu Abubakar, ya ce yana jiran cikakken rahoton jami’in ‘yan sanda na Jega kafin ya sanar da manema labarai.

RN

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *