Daliban Jami’ar Maryam Abacha MAAUN Sun Kirkiri Manhajar Sada Zumunta

IMG 20240114 WA0195

Tsofaffin daliban Jami’ar Maryam Abacha American University dake Maradi a jamhuriyyar Nijer sun bayyana cewa sun kirkiri wata manhaja wacce al’umma za su yi amfani da ita wajen sada zumunta a tsakaninsu.

Alfijir labarai ta rawaito Manhajar wacce suka sanya wa suna da ‘Afrister’, sun ce manhaja ce da aka kirkira da za ta kawo sauyi wajen bai wa al’ummar damar kulla alaka da huldar zamantakewa.

Sun kara da cewa an tsara manhajar ta yadda za ta haɓaka hulda a tsakanin daidaikun mutane, iyalai, abokai, da abokan kasuwanci, wanda zai haɓaka ƙwarewar masu amfani da manhajar.

An kirkiri manhajar ne a cikin shekarar 2021, a lokacin da Aliyu Ishaq da abokin aikinsa Alhassan Abubakar suke karatunsu a jami’ar MAAUN.

A cewarsu Afrister ya sami karbuwa cikin sauri a wurin masu amfani da shi ganin yadda manhajar ta zo da sabbin abubuwa masu kayatarwa.

A wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja, Aliyu Ishaq ya danganta nasarar Afrister da irin horon da suka samu a jami’ar Maryam Abacha.

Ya nuna matukar godiyarsa ga jami’arsa da ya kammala, inda ya bayyana irin tasiri da jami’ar ta yi masa tare da sauran dalibai.

Ya kuma yabawa wanda ya assasa jami’ar ta MAAUN, Farfesa Adamu Gwarzo bisa irin goyon baya da jagorancin da yake bayarwa.

Domin ganin sun samu yabo da karbuwa a duniya, Ishaq da abokin aikinsa sun ce suna aiki tuƙuru domin haɓaka Afrister, tare da tabbatar da cewa ya dace da ƙa’idodin da takwarorinsa na Yamma suka gindaya.

Ya kara da cewa, suna da himma da kuma kudurin yada Afrister a duniya, wanda ya ce idan suka yi hakan, za su samu wani gagarumin ci gaba a bangaren masana’antar fasaha da manhajar kulla zamantakewa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *