Dalilan Da Ya sanya Masu Zuba Jari Na Waje Ke Gujewa Nijeriya -Atiku Abubakar

FB IMG 1704886903715

Dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abuabar, ya bayyana cewa masu zuba jari daga kasashen waje za su ci gaba da kauracewa Najeriya muddin Gwamnati mai ci ta dogara da farfaganda maimakon mayar da hankali wajen jawo masu zuba jari na gaskiya.

Alfijir labarai ta rawaito a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya fitar a Abuja A ranar Lahadi, Atiku ya shawarci shugaba Tinubu da ya ba da fifiko wajen jawo masu zuba jari na hakika

Atiku ya bayyana damuwarsa kan bada aikin babbar hanyar Legas zuwa Calabar ga kamfanin Hitech mallakin Chagoury, wanda ake zargin na Tinubu ne. Ya kuma soki yadda ake gudanar da aikin, wanda ya bayyana a matsayin aikin Gwamnati mafi tsada da aka taba gudanarwa a Najeriya.

Ya kara da bayyana rugujewar  wuraren yawon bude ido da na shakatawa a cikin titin Oniru, da suka haɗa da wasu sassan Landmark, a matsayin wani abu da ke kawo kasala wajen jawo hannun jarin ƙasashen waje (FDI).

Daga karshe ya soki Gwamnatin Tinubu da fifita sha’anin kasuwanci na kashin kai fiye da bukatun kasa da kasa inganta saukin kasuwanci. Atiku ya ba da misali da rashin daidaito, rashin gaskiya, da kuma rashin bin ka’idojin tsare-tsare a ayyuka da manufofi daban-daban a karkashin jagorancin Tinubu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *