Dalilan Da Yasa Har Yanzu Sojojin Ecowas Ba Su Afkawa Nijar Ba – Tuggar

Ya zuwa yanzu za a iya cewa an kai wani mataki na kiki-kaka a yunƙurin mayar da mulkin demokuraɗiyya a jamhuriyar Nijar.

Sojojin da suka yi iƙirarin ƙwace mulki a ƙasar sun ƙi martaba umarnin Ecowas na mayar da Mohamed Bazoum kan kujerarsa.
Yayin da Ecowas ta dage kai da fata cewa wajibi ne a sojojin su kauce daga mulki.

Manyan hafsaoshin soji na ƙasashen yankin, a zamansu na ƙarshe da suka yi a Ghana sun bayyana cewa sun tsayar da lokacin kai samame a Nijar domin mayar da Bazoum kan muƙaminsa, sai dai ba su bayyana ranar ba.

Tun farko ƙungiyar ta Ecowas ta sha alwashin cewa za ta ɗauki matakin soji a kan Nijar matuƙar sojojin ba su saki shugaban ƙasar tare da mayar da shi kan mulki ba.

Sai dai duk barazanar da Ecowas ɗin ta yi, sojojin sun yi biris, har ma sun bayyana cewa tsarinsu shi ne su mayar da mulki ga farar hula bayan shekara uku, wani mataki da ƙasashen na Ecowas suka yi watsi da shi.

A tattaunawarsa da BBC, ministan harkokin waje na Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar ya ce dalilin da ya sa ake ci gaba da jan ƙafa kan ɗaukan matakin soji a kan Nijar shi ne, domin bayar da damar ganin ko za a iya warware rikicin ta hanyar tattaunawa.

Ya ce “Abu ne da abubuwa da dama suna faruwa kuma ana la’akari da zaman lafiya shi yasa ka ga ba ɗauki wasu matakai ba.”

Sau biyu dai tawagar Ecowas ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Abdulsalami Abubakar ta gana da jagororin juyin mulkin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *