Dalilin da yasa har yanzu ban kara aure ba! Inji Tsohon Shugaban Kasa Babangida

 Dalilin da yasa har yanzu ban kara aure ba – Inji IBB 

Best Seller Channel 

Best Seller Channel 

Tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya bayyana dalilin da yasa bai auri wata mata ba tun bayan rasuwar matarsa, Hajiya Maryam Babangida.

 IBB, mai shekaru 80, ya kuma yi magana kan irin shugaban da yake so wa Najeriya a 2023. 

Tsohon shugaban na mulkin sojan ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da yayi da gidan talabijin na Trust. 

Best Seller Channel 

Maryam Babangida ta rasu ne a ranar 27 ga Disamba, 2009, tana da shekaru 61. 

Maryam, wadda ta kasance Uwargidan Shugaban Najeriya a tsakanin 1985 zuwa 1993, ta rasu a Jami’ar California ta Jonsson Comprehensive Cancer Centre (JCCC) da ke Los Angeles, Amurka, bayan ta yi fama da cutar kansar Ovarian. tsawon shekaru. 

Tun bayan rasuwarta sama da shekaru 12 da suka gabata ‘yan Najeriya da dama sun yi tunanin cewa IBB zai auri wata mata domin ya ci gaba da zama da ita, amma hakan bai samu ba har yau. 

Best Seller Channel 

A wani lokaci, an yi ta rade-radin cewa IBB zai auri sabuwar mata amma bai yi ba. 

Amma da aka tambaye shi a wata hira ta baya-bayan nan dalilin da ya sa bai auri wata mata shekaru da yawa bayan rasuwar Hajiya Maryam, IBB ya ce: Lokaci yasa. 

Slide Up
x