Dan Sanda Ya Kashe Abokin Aikinsa Ya Kuma Harbe Kansa

Wani dan sanda mai mukamin Sufeto ya kashe abokin aikinsa sannan ya harbe kansa har lahira

Alfijir labarai ta rawaito lamarin ya faru ne ranar Lahadi a kauyen Nyogor-Lueku, Karamar Hukumar, Jihar Ribas.

Aminiya ta samu bayani cewa ’yan sandan biyu suna aiki ne a caji ofis da ke Taabaa, lokacin da suka tafi aiki Nyogor-Lueku su kamo wani mutum bisa wasu tuhume-tuhume da mahaifiyarsa ta kawo kara ofishin.

Kazalika ana zargin sa da bijire wa umarnin gayyatar da aka yi masa, al’amarin da ya kawo ce-ce-ku-ce tsakaninsa da jami’an.

Majiyar labarinmu ta ce “Ana tsaka da wannan cacar baka sai cikin kuskure Sufeto Nelson Abuante ya yi jarbi ya samu abokin aikinsa Gbaramana, ya ji mummunan rauni

“A sakamakon haka sai Abuante da mahaifiyar mutum da aka je kawa suka gaggauta daukar sa zuwa asibiti a cikin mota, amma sai mai ya kare a hanya, ta wannan dalili me Sufeto Monday ya ce ga garin ku nan.

“Har-wa-yau ganin abokin aikinsa ya mutu, shi ma Sufeto Abuante ba tare da jinkiri ba ya sanya bindigarsa ya harbe kansa.”

Wakilin mu ya tuntubi kakakin rundunar Grace Iringe-Koko, kuma ta tabbatar da hakan ya afku, ta kara da cewa “An kafa kwamitin bincike a kan lamarin.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *