Dr Maryam Abacha Ta Yi Kira Ga Gwamnatoci Da Su Tallafawa Mabuƙata Da Kayayyakin Abinci

IMG 20240304 WA0055

Hajiya (Dr) Maryam Abacha, Uwargidan tsohon shugaban ƙasar Nijeriya, Marigayi Sani Abacha ta yi kira ga gwamnoni da sauran al’umma masu ƙarfi da su siya kayayyakin abinci su tallafawa al’umma marasa ƙarfi musamman a daidai wannan lokaci da ake fuskantar watan Ramadan.

Alfijir labarai ta rawaito Hajiya Maryam ta bayyana hakan ne ga manema labarai a gidanta dake birnin Kano a yayin addu’ar tunawa da shekara ɗaya da rasuwar ɗanta Abdullahi.

Hajiya Maryam ta lura da cewa al’umma a halin yanzu suna cikin wani yanayi da suke da matuƙar buƙatar taimako. Inda ta ja hankalin musamman gwamnoni da su yi amfani da ƙarin kuɗaɗen da gwamnatin Tarayya ta ba su wajen hidimtawa al’umma.

“Ina kira ga gwamnatoci da al’umma da su taimaka ma jama’a. A gaskiya akwai rashin kuɗi. Akwai abinci amma ya yi tsada ga ƙarancin kuɗi”, in ji ta.

Ta ci gaba da cewa; “Don Allah jama’a a taimaka. Masu kuɗi, masu gwamnati su taimaka. Kuma na ji daɗi sosai da aka ce shugaban ƙasa ya ba gwamnoni kuɗi da yawa. Allah yasa su yi amfani da shi yadda ya dace. A siya hatsi da amfani a raba ma marasa ƙarfi a cikin al’umma”.

Ta ƙara da cewa; “masu ƙarfi kowa ya yi ƙoƙari ya harhaɗa ya tallafa. Haka addinin Musulunci ya ce, haka addinin kirista ya ce. Ka ga kowa zai samu idan aka yi hakan. Allah yasa a yi.”

Ta ci gaba da cewa; “kuma Allah ya taimaki al’ummarmu na Arewa da Nijeriya baki ɗaya. Allah ka taimaki ɗan Adam na duniya gaba ɗaya. Gaskiya duniya tana cikin matsala, ƙasa tana cikin matsala. Allah ya agaza mana ya dafa mana, kuma ya taimaka mana. Allah ya ba mu lafiya da zama lafiyarmu, kuma Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya da abin da za mu ci duka”.

Ta yi addu’ar Allah ya sa mu riski watan Ramadan da rai da lafiya, inda ta ce; “watan Ramadan da mai rai da lafiya kullum shekara ana yi. Allah yasa mu samu wannan lafiya, da ranmu da lafiyarmu yasa a yi damu”, ta jaddada.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *