Kotu ta Yanke Hukunci Kan Karar da Ganduje Ya Kai Akan Video Din Dala

Screenshot 20240305 180331 com.twitter.android edit 1235495393040

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke hukuncin cewa hukumar karbar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ba ta da hurumin gudanar da bincike kan zargin karbar cin hanci da akewa tsohon gwamna Abdullahi Ganduje a wani bidiyon.

Alfijir labarai ta rawaito alkalin kotun, Mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman a ranar Talata ya yanke hukuncin cewa laifin yana karkashin dokar tarayya da hukumar jihar ba ta da iko a kai.

Idan dai za a iya tunawa, Abdullahi Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano ya maka hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano a gaban kotu inda ya bukaci alkalai da su dakatar da binciken bidiyon dala da hukumar ta ce zata yi masa.

Sai dai Lauyan wanda ake kara na farko a karar, Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano Barr. Usman Umar Fari ya ce za su daukaka kara kan hukuncin kotun.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *